Posts

Yadda zaka iya amfani da UBA MAGIC BANKING a kyauta

Image
Yadda zaka iya amfani da UBA MAGIC BANKING a kyauta Assalamu alaikum, Barkan ku da yau sannunku da sake saduwa da wannan blog wato Amarawa Online. A yau kasidar tamu za kawo maku wata hanya ce yadda zaku iya gudanar da harkokin na bankin United Bank for Africa wato UBA da wayar tafi da gidan ka, a kyauta batare da an dauki ko kobo alayin ka na waya ba. Kasancewar Shekarun baya da suka gabata bankin UBA ya kirko da wani tsari na sa mai suna UBA MAGIC BANKING, wanda yake baiwa masu mu'amala da bankin damar guda nar da harkokin asusun ajiyar su wato Transactions ta hanyar amfani da wayar sa ta salula, batare da yaje wani daga cikin reshen bankin ba, ko zuwa waje ATM machine ba, kawai abun da kake buka wayar hannu komai kankantar ta, layin waya amma ka tabbata layin da kake karbar sakon karta kwana ne wato sms alert daga bankin. sai kayi amfani da USSD CODES da suka samar wato *919# . Sai ya kasance bankin suna daukar ladar dawainiyar kowane transaction da kayi kamar, checki...

Yadda ake raba Hard Disk na Comuter - Yadda Ake Hard Disk Portitioning

Image
Yadda ake raba Hard Disk na Comuter - Yadda Ake Hard Disk Portitioning Assalamu alaikum, Barkan ku da yau sannunku da sake saduwa a wannan dandali na Amarawa Online. Yau cikin yardar Allah zamu kawo kasidar mu akan akan yadda ake raba memory na computerwto disk partitioning MENENE DISK PARTITIONING? Disk Portitioningna nufin rarraba ko ince karkasa memory na computer zuwa kashi-kashi. Idan muka lura da kwamfiyutoci na mutane daban daban zamuga wadansu kwamfiyutocin zamuga hard disk din su guda dayane tak, wadansu kuwa kashi kashine Musamman ma ga masu amfani da Laptop, wacce daman sanin kowa ne Hard Disk daya take dauke dashi. Nasan mai tambaya kan iya tambayar cewar to ya akeyi hakan na faruwa? Eh, hakan na faruwa ne sakamako Partition da ake yi ma wannan disk din.Mutane da dama ba susan amfanin Disk partitition ba shiyasa ba su damu da suga sun raba disk din nasu ba, duk da cewar dai yin hakan nada matukar amfani AMFANIN DISK PARTITION Hard Disk na computer acikin sa...

Amfanin Google Drive

Image
YAYA AKE AMFANI DA GOOGLE DRIVE? MENENE GOOGLE DRIVE? Google Drive wata ma'adana ce , wadda kamfanin Google ya kirkirota a aranar ashirin da hudu da watan afrilun dubu biyu da sha biyu 24 April, 2012. Kamfanin na Google ya kirkiro wannan ma'ajiyar ce domin ya baiwa abokan huddarsa damar dorawa da saukewa, ajiya da kuma rarraba kayayyakin su, wadanda suka shafi bayanai da kayayyaki irin na na'urorin wayoyi da kwamfiyuta (files da softwares), wadanda da suka kunshi; hotuna, hotunan bidiyo, sautuka na murya, manhajoyin wayoyi da kwamfiyotoci, a jikin uwar garken kamfanin na google wato Google server kuma a kyauta. Wannan kusan ace itace dama ta farko da wani kamfanin yanar gizo ya taba baiwa masu hulda da shi atsawon tarihi, kasancewar dukkan wani mai ta'ammali da kafar sadarwar yanar gizo ya san makudan kudin da mutan kan biya, domin adana masa bayanan sa a yanar ta gizo, musamman bayanai masu nauyi. Ana cikin wannan halin ne Google ya kawo wannan garabasa, inda y...

YADDA AKE KIRKIRAR GROUP LINK A DANDALIN WHATSAPP

Image
      Sanin kowa ne musamman masu amfani da dandalin whatsapp cewar, Whatsapp group zaure ne da ake amfani dashi domin tattaro mabanbantan mutane daga mabanbantan wurare, da zummar kasancewa awuri daya domin tattauna babutuwan da ake bukatar tattaunawa. Wadan su zaurukan  suna kasancewa ne na abokai zalla, wasu kuma na addini, wasu na siyasa, wadansu kuma abokan karaatu ne kawai ke acikin shi. Wadan su mutanen kuwa,kan kirkira zaurukan whatsapp ne amatsayin Aji na daukarkar darassu awani daga cikin bangare na Ilimi, musamman ga masu koyo da koyarwa a yanar gizo wato E-Learning. Whatsapp group yanada tsari kamar sauran zaurukan sada zumunta, a inda ya kasance akwai ADMIN wato mai kula da zauren, Shine yake da damar sakawa ko cire mutum a wannan zaure. wani ko wata ba zai iya zamowa member a wannan group din ba, har sai ya mika bukatar hakan zuwa ga admin sannan admin ya almunce masa ya saka shi awan nan group din. Akwai lokacin da mutum ke son Gayyata...